Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Families: Of saints blessed
Ayoyi game da Of saints blessed
Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.
Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.
Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,
bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.