Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Faithfulness

6 ayoyi · 35 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba.

  2. In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya?

  3. In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku?

  4. A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum.

  5. Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba.

  6. ’Yan’uwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki