Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Dumb

6 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana.

  2. Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba.”

  3. Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su.

  4. Mutanen kuwa suka yi mamaki sa’ad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Isra’ila.

  5. Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, “Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.”

  6. Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.”