Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Divisions

6 ayoyi · 10 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ina so dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni.

  2. Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya.

  3. Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni.

  4. ’Yan’uwana, waɗansu daga iyalin gidan Kulos sun gaya mini cewa, akwai faɗa a cikinku.

  5. Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.”

  6. Kiristi a rabe ne? Bulus ne aka gicciye dominku? An yi muku baftisma a cikin sunan Bulus ne?