Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Contentment: General references

15 ayoyi · 13 fannoni

Ayoyi game da General references

  1. Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai.

  2. Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.

  3. Dukan ƙoƙarin da mutum yake yi, yana yi ne domin bakinsa, duk da haka bai taɓa gamsar da abin da yake marmari.

  4. Da me mai hikima ya fi wawa? Wace riba ce matalauci yakan samu don yă iya zama da mutane?

  5. Gara abin da ido ya gani da kwaɗayin da bai sami biyan bukata ba. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.

  6. Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da farin zuciya, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.

  7. Kullum ka kasance cikin farin riguna, ka kuma shafe kanka da mai kullum,

  8. Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya.

  9. Ya kamata kowa yă kasance a matsayin da yake ciki sa’ad da Allah ya kira shi.

  10. Kai bawa ne sa’ad da aka kira ka? Kada wannan yă dame ka, sai dai in kana iya samun ’yanci, sai ka yi amfani da wannan dama.

  11. Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali.

  12. Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara.

  13. Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa.

  14. Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba.

  15. In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su.