Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Conscience

64 ayoyi · 15 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?

  2. Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.

  3. Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah

  4. Da a ce za tă iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtacce masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba.

  5. Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara,

  6. domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai ba.

  7. Saboda haka, sa’ad da Kiristi ya shigo duniya ya ce, “Hadaya da sadaka kam ba ka so, sai dai ka tanadar mini jiki;

  8. hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin.

  9. Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ”

  10. Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su).

  11. Sa’an nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yă kafa na biyun.

  12. Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak.

  13. Idan zuciyarmu ta nuna mana muna da laifi, mun san cewa Allah ya fi zuciyarmu, ya kuma san dukan kome.

  14. Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan.