Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Christian Graces

27 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu, gama mulkin sama nasu ne.

  2. Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu ta’aziyya.

  3. Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u, gama za su gāji duniya.

  4. Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci, gama za a ƙosar da su.

  5. Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.

  6. Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.

  7. Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ’ya’yan Allah.

  8. Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci, gama mulkin sama nasu ne.

  9. “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.

  10. Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri;

  11. jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege.

  12. Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

  13. In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai.

  14. In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne.

  15. In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

  16. Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai.

  17. Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya.

  18. Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya.

  19. Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

  20. Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare.

  21. Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci,

  22. sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

  23. Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani;

  24. ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah;

  25. ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna.