Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Beriah: 2. Son of Ephraim
Ayoyi game da 2. Son of Ephraim
Zuriyar Efraim su ne, Shutela, Bered, Tahat, Eleyada, Tahat
Zabad da Shutela. Wani ɗan ƙasa haifaffen mutanen Gat ya kashe Ezer da Elad, sa’ad da suka gangara don su ƙwace dabbobinsu.
Mahaifinsu Efraim ya yi makoki dominsu kwanaki masu yawa sai danginsa suka zo don su yi masa ta’aziyya.
Sa’an nan ya sāke kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Beriya, saboda masifar da ta auko a cikin iyalinsa.