Skip to content

Hermon

7 verses

33.4100, 35.8500 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Hermon

  1. A lokacin ne muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato, ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga Kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon.

  2. Daga Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa wajajen Seyir, zuwa Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon ƙasa da Dutsen Hermon. Ya kama sarakunansu ya karkashe su.

  3. Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba.

  4. Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.

  5. da ƙasar Gebaliyawa; da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba’al-Gad a gindin Dutsen Hermon zuwa Lebo Hamat.

  6. Haɗe da Gileyad, inda mutanen Geshur da Ma’aka suke. Dukan Dutsen Hermon, da dukan Bashan har zuwa Saleka,

  7. Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon).