Skip to content

Amon

15 ayoyi · 4 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Amon

  1. Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a lambun fadansa, lambun Uzza. Sai Amon ɗansa ya gāje shi.

  2. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet ’yar Haruz; ita mutuniyar Yotba ce.

  3. Fadawan Amon suka ƙulla maƙarƙashiya suka kashe shi a cikin fadarsa.

  4. Sai mutanen ƙasar suka kashe duk waɗanda suka ƙulla wa Sarki Amon maƙarƙashiya, sa’an nan suka naɗa ɗansa sarki a maimakonsa.

  5. Game da sauran ayyukan mulkin Amon, da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

  6. da Amon, da Yosiya.

  7. Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a fadansa. Sai Amon ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  8. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki a Urushalima shekara biyu.

  9. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda mahaifinsa Manasse ya yi. Amon ya bauta ya kuma miƙa hadayu ga dukan gumakan da Manasse ya yi.

  10. Amma ba kamar mahaifinsa Manasse ba, bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji ba; Amon ya ƙara laifinsa.

  11. Sa’an nan mutanen ƙasar suka kashe dukan waɗanda suka yi wa Sarki Amon maƙarƙashiya, suka naɗa Yosiya ɗansa sarki a maimakonsa.

  12. Maganar Ubangiji ta zo gare shi a shekara ta goma sha uku ta sarautar Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda,

  13. Shekaru ashirin da uku, daga shekara ta goma sha uku ta Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda har zuwa wannan rana, maganar Ubangiji ta zo mini na kuma yi muku magana sau da sau, amma ba ku saurara ba.

  14. Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda.

  15. Hezekiya ya haifi Manasse, Manasse ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya,