Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Amon

14 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a lambun fadansa, lambun Uzza. Sai Amon ɗansa ya gāje shi.

  2. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet ’yar Haruz; ita mutuniyar Yotba ce.

  3. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda Manasse mahaifinsa ya yi.

  4. Ya bi duk gurbin mahaifinsa a kome, ya yi sujada ga gumakan da mahaifinsa ya yi wa, ya kuma durƙusa musu.

  5. Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai kuwa yi tafiya a hanyar Ubangiji ba.

  6. Fadawan Amon suka ƙulla maƙarƙashiya suka kashe shi a cikin fadarsa.

  7. Sai mutanen ƙasar suka kashe duk waɗanda suka ƙulla wa Sarki Amon maƙarƙashiya, sa’an nan suka naɗa ɗansa sarki a maimakonsa.

  8. Game da sauran ayyukan mulkin Amon, da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

  9. Aka binne shi a kabarinsa a lambun Uzza. Yosiya ɗansa kuma ya gāje shi.

  10. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki a Urushalima shekara biyu.

  11. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda mahaifinsa Manasse ya yi. Amon ya bauta ya kuma miƙa hadayu ga dukan gumakan da Manasse ya yi.

  12. Amma ba kamar mahaifinsa Manasse ba, bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji ba; Amon ya ƙara laifinsa.

  13. Fadawan Amon sukan yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a fadansa.

  14. Sa’an nan mutanen ƙasar suka kashe dukan waɗanda suka yi wa Sarki Amon maƙarƙashiya, suka naɗa Yosiya ɗansa sarki a maimakonsa.