Zefaniya 3:8
Ana nuna aya 8 tare da mahallin da ke kewaye.
5
Ubangiji da yake cikinki mai adalci ne; ba ya yin abin da ba daidai ba. Kowace safiya yakan bayyana dokokinsa a fili, kowace sabuwar rana kuma ba ya kāsawa, duk da haka marasa adalci ba sa jin kunya.
6
“Na daddatse al’ummai; an kuma rurrushe kagararsu. Na bar titunansu ba kowa, ba mai ratsawa a ciki. An ragargaza biranensu; ba wanda za a bari, babu ko ɗaya.
7
Na ce wa birnin, ‘Tabbatacce za ki ji tsorona ki kuma yarda da gyara!’ Ta haka ba za a datse wurin zamanki ba, ba kuwa dukan hukuncena za su hau bisa kansu ba. Amma har yanzu suna marmari su yi rashin gaskiya a duk abin da suke yi.
8
Saboda haka ku jira ni,” in ji Ubangiji; “a ranar da zan tsaya in ba da shaida, Na yanke shawara in tattara dukan al’ummai, in tattara mulkoki in kuma zuba fushina a kansu, da dukan zafin haushina. Za a mamaye dukan duniya da zafin fushina.
9
“Sa’an nan zan tsarkake leɓunan mutanen, don dukansu su kira bisa ga sunan Ubangiji su kuma yi masa hidima kafaɗa da kafaɗa.
10
Tun daga ƙetaren rafuffukan Kush masu yi mini sujada, mutanena da suke a warwatse, za su kawo mini hadayu.
11
A wannan rana ba za ku sha kunya saboda laifofin da kuka yi mini, gama zan ɗauke wa wannan birni waɗanda suke farin ciki cikin girmankansu. Ba kuma za ka ƙara yin kallon reni a tuduna mai tsarki ba.
Settings