Zakariya 8:13-23
13
Kamar yadda kuka zama abin la’ana a ƙasashe, ya Yahuda da Isra’ila, haka zan cece ku, za ku kuma zama albarka. Kada ku ji tsoro, sai dai ku bar hannuwanku su zama da ƙarfi.”
14
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Kamar dai yadda na yi niyyar kawo muku bala’i, in kuma ƙi jin tausayi sa’ad da kakanninku suka ba ni haushi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki,
15
kada ku ji tsoro “saboda a yanzu na yi niyya in sāke yi wa Urushalima da Yahuda abu mai kyau.
16
Abubuwan da za ku yi ke nan. Ku gaya wa juna gaskiya, ku kuma dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunanku na shari’arku;
17
kada ku ƙulla wa maƙwabtanku mugunta, kuma kada ku so yin rantsuwa ta ƙarya. Ina ƙyamar waɗannan duka,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
18
Maganar Ubangiji Maɗaukaki ta sāke zuwa wurina.
19
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Azumin wata na huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai da na watan goma za su zama lokutan farin ciki da murna da kuma bukukkuwa na murna ga Yahuda. Saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.”
20
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Mutane da yawa da kuma mazaunan birane da yawa har yanzu za su zo,
21
mazaunan wani birni za su je wurin mazaunan wani birni su ce, ‘Bari mu je nan da nan mu roƙi Ubangiji mu kuma nemi Ubangiji Maɗaukaki. Ni kaina zan je.’
22
Mutane da yawa kuma da al’ummai masu ƙarfi za su zo Urushalima su nemi Ubangiji Maɗaukaki su kuma roƙe shi.”
23
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “A kwanakin nan, mutane goma daga kabilu da al’ummai za su riƙe rigar mutumin Yahuda guda su ce, ‘Bari mu tafi tare da kai, domin mun ji cewa Allah yana tare da ku.’ ”
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings