Waƙar Waƙoƙi 7:1-9
1
Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne, Ya diyar sarki! Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja, aikin hannun gwanin sassaƙa.
2
Cibinki kamar kwaf ne da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba. Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama wanda furen bi-rana ya kewaye.
3
Nonanki sun yi kamar bareyi biyu, tagwayen barewa.
4
Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon kusa da ƙofar Bat Rabbim. Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon wadda take duban Damaskus.
5
Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel. Gashinki ya yi kamar shunayya; yakan ɗauke hankalin sarki.
6
Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi, Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!
7
Tsayinki ya yi kamar itacen dabino, kuma nonanki sun yi kamar ’ya’yan itace.
8
Na ce, “Zan hau itacen dabino; zan kama ’ya’yansa.” Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa, ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa,
9
kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau. Ƙaunatacciya Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena, yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.
Settings