Waƙar Waƙoƙi 7:10-13
10
Ni ta ƙaunataccena ce, kuma sha’awarsa domina ne.
11
Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari, bari mu kwana a ƙauye.
12
Bari mu tafi gonar inabi da sassafe don mu ga ko kuringar ta yi ’ya’ya, ko furanninsu sun buɗe, ko rumman sun yi fure, a can zan nuna maka ƙaunata.
13
Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu, a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi, sabo da tsoho, da na ajiye dominka, ƙaunataccena.
Settings