Waƙar Waƙoƙi 8:1-4
1
Da a ce kai ɗan’uwa ne gare ni, wanda nonon mahaifiyata sun shayar! Da in na same ka a waje, na sumbace ka, babu wanda zai rena ni.
2
Da sai in bi da kai in kawo ka gidan mahaifiyata, ita da ta koyar da ni. Da na ba ka ruwan inabi gaurayayye da kayan yaji ka sha, zaƙin rumman nawa.
3
Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni.
4
’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.
Settings