Skip to content
Romawa 11:11-24

Romawa 11:11-24

11
Har yanzu ina da tambaya. Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Al’ummai don a sa mutanen Isra’ila su ji kishi.
12
Amma in laifinsu yana nufin albarka ga duniya, hasararsu kuma albarka ga Al’ummai, ina misalin yalwar da albarkunsu za su kawo!
13
Ina magana da ku ne fa Al’ummai. Tun da yake ni manzo ne ga Al’ummai, ina taƙama da aikin nan nawa,
14
da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yă sa in ceci waɗansunsu.
15
Gama in ƙinsu da aka yi ya zama sulhu ga duniya, me karɓarsu za tă zama in ba rai daga matattu ba?
16
In sashen da aka miƙa a matsayin nunan fari tsattsarka ne, to, sauran ma tsattsarka ne; in saiwar tsattsarka ce, to, sauran rassan ma tsattsarka ne.
17
In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,
18
kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi la’akari da wannan. Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka.
19
To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.”
20
Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro.
21
Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.
22
Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka.
23
In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su.
24
Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options