Skip to content
Zabura 85:1-9

Zabura 85:1-9

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji; ka mai da nasarorin Yaƙub.
2
Ka gafarta laifin mutanenka ka kuma shafe dukan zunubansu. Sela
3
Ka kau da dukan fushinka ka kuma juye daga hasalar fushinka.
4
Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.
5
Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?
6
Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?
7
Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji, ka kuma ba mu cetonka.
8
Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa; ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa, amma kada su koma ga wauta.
9
Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa, don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options