Zabura 45:9-12
9
’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama; a hannun damarka kuwa ga amarya, sarauniya saye da ofir zinariya.
10
Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne, Ki manta da mutanenki da gidan mahaifinki.
11
Sarki ya cika da sha’awar kyanki; ki girmama shi, gama shi ne maigidanki.
12
Diyar Taya za tă zo da kyauta, mawadata za su nemi tagomashinki.
Settings