Zabura 44:3-10
3
Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar, ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba; hannun damanka ne, ƙarfin hannunka, da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su.
4
Kai ne Sarkina da kuma Allahna, wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub.
5
Ta wurinka mun tura abokan gābanmu baya; ta wurin sunanka muka tattake maƙiyanmu.
6
Ba na dogara ga bakana, takobina ba ya kawo nasara;
7
amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu, ka sa abokan gābanmu suka sha kunya.
8
A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini, kuma za mu yabi sunanka har abada. Sela
9
Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu; ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.
10
Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba, kuma abokan gābanmu suka washe mu.
Settings