Zabura 37:34-40
34
Ku sa zuciya ga Ubangiji ku kuma kiyaye hanyarsa. Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar, sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani.
35
Na ga wani mugu, azzalumi, yana yaɗuwa kamar ɗanyen itace a asalin ƙasarsa,
36
amma yakan mutu nan da nan kuma ba ya ƙara kasancewa; ko an neme shi, ba za a same shi ba.
37
Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali; akwai sa zuciya domin mutum mai salama.
38
Amma za a hallaka dukan masu zunubi; za a yanke sa zuciya ta mugaye.
39
Ceton adalai kan zo daga Ubangiji; shi ne mafaka a lokacin wahala.
40
Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su; yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su, domin sukan nemi mafaka daga gare shi.
Settings