Skip to content
Zabura 37:21-33

Zabura 37:21-33

21
Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya, amma masu adalci suna bayar hannu sake;
22
waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka za su gāji ƙasar, amma waɗanda ya la’anta, za a kore su.
23
In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi, zai sa sawu su kahu;
24
ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.
25
Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.
26
Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa ’ya’yansu albarka.
27
Ku juyo daga mugunta ku yi alheri; sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada.
28
Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai kuma ba zai yashe amintattunsa ba. Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya, ’ya’yan mugaye za su hallaka.
29
Masu adalci za su gāji ƙasar su kuma zauna a cikinta har abada.
30
Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima, harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.
31
Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa; ƙafafunsa ba sa santsi.
32
Mugaye suna fako suna jira masu adalci, suna ƙoƙari neman ransu;
33
amma Ubangiji ba zai bar su a ikonsu ba ko ya bari a hukunta su sa’ad da aka kawo su shari’a ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options