Zabura 37:12-20
12
Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya su ciji baki a kansu;
13
amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa.
14
Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke.
15
Amma takubansu za su soki zukatansu, kuma bakkunansu za su kakkarye.
16
Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi ya fi arzikin mugaye yawa;
17
gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci.
18
Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji, kuma gādonsu zai dawwama har abada.
19
A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba; a kwanakin yunwa za su sami a yalwace.
20
Amma mugaye za su hallaka, Abokan gāban Ubangiji za su zama kamar kyan gonaki, za su ɓace, za su ɓace kamar hayaƙi.
Settings