Skip to content
Zabura 31:14-24

Zabura 31:14-24

14
Amma na dogara gare ka, ya Ubangiji; na ce, “Kai ne Allahna.”
15
Lokutana suna a hannuwanka; ka cece ni daga abokan gābana da kuma daga waɗanda suke fafara ta.
16
Bari fuskarka ta haskaka a kan bawanka; ka cece ni da ƙaunarka marar ƙarewa.
17
Kada ka bari in sha kunya, ya Ubangiji, gama na yi kuka gare ka; amma bari mugaye su sha kunya su kuma kwanta shiru a cikin kabari.
18
Bari a rufe leɓunan ƙarairayinsu, gama da fariya da reni suna magana da girman kai a kan adalai.
19
Alherinka da girma yake, wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka, wanda ka mayar a gaban mutane a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka.
20
Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su daga makircin mutane; a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya daga harsuna masu zagi.
21
Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya nuna ƙaunarsa mai banmamaki gare ni sa’ad da aka yi mini kwanto kewaye da birni.
22
Cikin tsorona na ce, “An yanke ni daga gabanka!” Duk da haka ka ji kukata na neman jinƙai sa’ad da na kira gare ka don taimako.
23
Ku ƙaunaci Ubangiji, dukanku tsarkakansa! Ubangiji yakan adana amintattu, amma masu girman kai yakan sāka musu cikakke.
24
Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa, dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options