Skip to content
Zabura 22:1-21

Zabura 22:1-21

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda. Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Me ya sa ka yi nisa da cetona, ka yi nesa daga kalmomin nishina?
2
Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba, da dare kuma ban yi shiru ba.
3
Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan; kai ne yabon Isra’ila.
4
A gare ka ne kakanninmu suka sa bege; sun dogara ka kuwa cece su.
5
Sun yi kuka gare ka suka kuma sami ceto; a gare ka suka dogara kuma ba su sha kunya ba.
6
Amma ni dai tsutsa ne ba mutum ba, wanda mutane suke yi wa ba’a suka kuma rena shi.
7
Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a; suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa,
8
“Ya dogara ga Ubangiji; bari Ubangiji yă cece shi. Bari yă cece shi, da yake yana jin daɗinsa.”
9
Duk da haka ka fitar da ni daga ciki; ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata.
10
Daga haihuwa an jefa ni a kanka; daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.
11
Kada ka yi nesa da ni, gama wahala na kusa kuma babu wani da zai taimaka.
12
Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.
13
Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama sun buɗe bakunansu a kaina.
14
An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina.
15
Ƙarfina ya bushe kamar kasko, harshena kuma ya manne wa dasashina na sama; ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa.
16
Karnuka sun kewaye ni; ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka, sun soki hannuwana da ƙafafuna.
17
Zan iya ƙirga ƙasusuwana; mutane suna farin ciki a kaina.
18
Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.
19
Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa; Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni.
20
Ka ceci raina daga takobi, raina mai daraja daga ikon karnuka.
21
Ka cece ni daga bakin zakoki; ka cece ni daga ƙahonin ɓauna.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options