Tsallake zuwa abun ciki
Zabura 17:1-7

Zabura 17:1-7

1
Addu’a ce ta Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, roƙona na adalci; ka saurari kukata. Ka kasa kunne ga addu’ata, ba ta fitowa daga leɓuna masu ƙarya.
2
Bari fiffitawata tă zo daga gare ka; bari idanunka su ga abin da yake daidai.
3
Ko ka duba zuciyata, ka kuma bincike ni da dare, ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba; na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.
4
Game da ayyukan mutane kuwa, ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina daga hanyoyin tashin hankali.
5
Sawuna sun kama hanyoyinka ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba.
6
Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini; ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata.
7
Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki, kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu da hannunka na dama.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options