Skip to content
Zabura 119:93-117

Zabura 119:93-117

93
Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina.
94
Ka cece ni, gama ni naka ne; na yi ƙoƙarin neman farillanka.
95
Mugaye suna jira su hallaka ni, amma zan yi ta tunani a kan farillanka.
96
Ga duk cikakke na ga kāsawa; amma umarnanka ba su da iyaka.
97
Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini.
98
Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni.
99
Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka.
100
Ina da ganewa fiye da dattawa, gama ina biyayya da farillanka.
101
Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka.
102
Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini.
103
Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina!
104
Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba.
105
Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata.
106
Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci.
107
Na sha wahala sosai; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka.
108
Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji, ka kuwa koya mini dokokinka.
109
Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana, ba zan manta da dokarka ba.
110
Mugaye sun kafa mini tarko, amma ban kauce daga farillanka ba.
111
Farillanka su ne gādona har abada; su ne farin cikin zuciyata.
112
Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka har ƙarshe.
113
Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka.
114
Kai ne mafakata da garkuwata; na sa zuciyata a maganarka.
115
Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna!
116
Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu; kada ka bari a gwale sa zuciyata.
117
Ka riƙe ni za a kuma cece ni; kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options