Skip to content
Filibbiyawa 4:14-23

Filibbiyawa 4:14-23

14
Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina.
15
Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai;
16
gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata.
17
Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku.
18
An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.
19
Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
20
Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin.
21
Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu. ’Yan’uwan da suke tare da ni suna gaishe ku.
22
Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar.
23
Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. Amin.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options