Filibbiyawa 3:4-11
4
ko da yake ni kaina ina da dalilan dogara da haka. In kuwa akwai wani wanda yake tsammani yana da dalilan dogara ga jiki, ni fa na fi shi,
5
an yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra’ila ne, na kabilar Benyamin, mutumin Ibraniyawa ɗan Ibraniyawa; bisa ga doka kuwa ni Bafarisiye ne;
6
wajen himma kuwa, ni mai tsananta wa ikkilisiya ne, wajen aikin adalci bisa ga hanyar doka, ni marar laifi ne.
7
Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi.
8
Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi
9
a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya.
10
Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa,
11
yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.
Settings