Obadiya 1:3-7
3
Fariyar zuciyarki ta yaudare ki, ke da kike zama can bisa duwatsu kika kuma yi gidanki a kan ƙwanƙoli, ke da kike ce wa kanki, ‘Wa zai iya saukar da ni ƙasa?’
4
Ko da yake kina firiya kamar gaggafa kin kuma yi sheƙarki a can cikin taurari, daga can zan saukar da ke,” in ji Ubangiji.
5
“In ɓarayi suka zo miki, in kuma ’yan fashi suka shigo gidan da dare, kash, bala’i zai jira ki ba abin da suke so ne kawai za su sata ba? In kuma masu tsinka ’ya’yan inabi suka zo miki, ba sukan bar ’ya’yan inabi kaɗan ba?
6
Amma za a washe Isuwa ƙaƙaf, a kuma yaye ɓoyayyiyar dukiyarsa!
7
Dukan waɗanda kike tarayya da su, za su kore ki zuwa iyaka; abokanki kuma za su yaudare ki, su kuma sha ƙarfinki; waɗanda suke cin abincinki, za su sa miki tarko, amma ba za ki gane ba.
Settings