Amos 9:11-15
11
“A wannan rana zan maido da tentin Dawuda da ya fāɗi. Zan gyaggyara wuraren da suka yayyage, in kuma maido da kufansa in gina shi kamar yadda yake a dā,
12
domin su mallaki raguwar Edom da duk al’ummai da suke amsa sunana,” in ji Ubangiji shi wanda zai yi waɗannan abubuwa.
13
“Ranaku suna zuwa, in ji Ubangiji, “sa’ad da mai huɗa zai sha gaban mai girbi mai shuki kuma yă bi bayan mai matsin inabi. Sabon ruwan inabi zai ɗiga daga duwatsu yă kuma kwararo daga tuddai.
14
Zan dawo da waɗanda aka kai zaman bauta mutanena Isra’ila. “Za su sāke gina biranen da suke kango su kuma zauna a cikinsu. Za su shuka gonakin inabi su kuma sha ruwan inabinsu; za su yi lambuna su kuma ci amfaninsu.
15
Zan dasa Isra’ila a ƙasarsu, ba kuwa za a ƙara tumɓuke su daga ƙasar da na ba su ba,” in ji Ubangiji Allahnku.
Settings