Nehemiya 6:1-9
1
Sa’ad da magana ta zo kunnen Sanballat, da Tobiya, da Geshem mutumin Arab da kuma sauran abokan gābanmu cewa na sāke gina katangar har babu sauran tsaguwa da ta ragu, ko da yake har zuwa lokacin ban sa ƙofofi a ƙyamare ba
2
Sanballat da Geshem suka aika mini wannan saƙo cewa, “Ka zo, mu sadu a wani ƙauye a filin Ono.” Amma makirci ne suke yi don su cuce ni;
3
saboda haka sai na aika musu da wannan amsa, na ce, “Ina cikin babban aiki, ba zan kuwa iya gangarawa ba. Don me zan bar aikin yă tsaya don in gangara zuwa wurinku?”
4
Suka yi ta aiko mini da wannan saƙo har sau huɗu, ni kuwa na yi ta ba su amsa irin ta dā.
5
Sai sau na biya, Sanballat ya aiki mataimakinsa gare ni da irin saƙo guda, kuma a hannunsa akwai wasiƙar da ba a yimƙe ba
6
wadda aka rubuta cewa, “An ba da labari cikin al’ummai, kuma Geshem ya ce gaskiya ne, cewa kai da Yahudawa kun shirya tawaye, saboda haka kuke sāke ginin katangar. Ban da haka ma, bisa ga waɗannan rahotanni kana shirin zaman sarkinsu
7
har ma ka naɗa annabawa su yi wannan shela game da kai a Urushalima, su ce, ‘Akwai sarki a Yahuda!’ To, wannan rahoto zai koma wurin sarki; saboda haka ka zo, mu tattauna wannan batu.”
8
Sai na aika masa wannan amsa, na ce, “Babu wani abu haka da yake faruwa; ka dai ƙaga wannan daga tunaninka ne.”
9
Suka dai yi ƙoƙari su tsoratar da mu, suna cewa, “Hannuwansu za su rasa ƙarfin yin aiki, ba kuwa za su ƙare aikin ba.” Amma na yi addu’a na ce, “Yanzu, ya Allah, ka ƙarfafa hannuwana.”
Settings