Nehemiya 6:10-14
10
Wata rana na tafi gidan Shemahiya ɗan Delahiya, ɗan Mehetabel, wanda aka hana fita a gidansa. Ya ce mini, “Mu sadu gobe a gidan Allah, a cikin haikali, mu kuma kulle ƙofofin haikali, gama mutane suna zuwa su kashe ka, tabbatacce za su zo da dare su kashe ka.”
11
Amma na ce, “Ya kamata mutum kamar ni yă gudu? Ko kuwa ya kamata wani kamar ni yă shiga cikin haikali don yă ceci ransa? Ba zan tafi ba!”
12
Na gane cewa Allah bai aike shi ba, ya yi annabci a kaina domin Tobiya da Sanballat sun yi hayarsa ne.
13
An yi hayarsa don yă sa in ji tsoro in yi zunubi ta yin haka, sa’an nan za su ba ni mugun suna, su wofinta ni.
14
Ya Allahna, ka tuna da Tobiya da Sanballat, saboda abin da suka yi; ka kuma tuna da annabiya Nowadiya da sauran annabawa waɗanda suke ƙoƙari su tsorata ni.
Settings