Skip to content
Nehemiya 2:11-18

Nehemiya 2:11-18

11
Sai na je Urushalima, bayan na zauna a can na kwanaki uku,
12
sai na fita da dare tare da mutane kalila. Ban faɗa wa wani abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi don Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau.
13
Da dare na fita ta Ƙofar Kwari wajen Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, ina dudduba katangar Urushalima waɗanda aka rushe da kuma ƙofofinta waɗanda aka ƙone da wuta.
14
Sa’an nan na ci gaba zuwa wajen Ƙofar Maɓuɓɓuga da kuma Tafkin Sarki, amma babu isashen wuri saboda abin da na hau yă bi;
15
saboda haka na haura ta kwarin da dad dare, ina dudduba katangar. A ƙarshe, na juya na sāke shiga ta Ƙofar Kwari.
16
Shugabanni ba su san inda na tafi, ko abin da nake yi ba, domin ban riga na faɗa wa Yahudawa, ko firistoci, ko manyan gari, ko shugabanni, ko sauran waɗanda za su yi aiki, kome ba.
17
Sai na ce musu, “Kun ga matsalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta da wuta. Ku zo mu sāke gina katangar Urushalima, ba za mu ƙara shan kunya ba.”
18
Na kuma faɗa musu game da yadda alherin Allahna yake tare da ni da kuma abin da sarki ya faɗa mini. Suka amsa, suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Sai suka fara wannan aiki mai kyau.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options