Mattiyu 9:9-15
9
Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.
10
Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa.
11
Sa’ad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da masu zunubi?”
12
Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
13
Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”
14
Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?”
15
Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi.
Settings