Skip to content
Mattiyu 3:1-12

Mattiyu 3:1-12

1
A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya
2
yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”
3
Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa, “Ga murya mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”
4
Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji.
5
Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun.
6
Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun.
7
Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?
8
Ku yi ayyukan da suka dace da tuba.
9
Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan.
10
An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.
11
“Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.
12
Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options