Skip to content
Mattiyu 26:26-35

Mattiyu 26:26-35

26
Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”
27
Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku.
28
Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.
29
Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”
30
Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
31
Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya saboda ni, gama a rubuce yake cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin, tumakin garken kuwa za su fasu.’
32
Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”
33
Bitrus ya amsa ya ce, “Ko da duka sun ja da baya saboda kai, ba zan taɓa ja da baya ba.”
34
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
35
Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options