Skip to content
Mattiyu 15:1-11

Mattiyu 15:1-11

1
Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce,
2
“Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!”
3
Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku?
4
Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’
5
Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’
6
ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku.
7
Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce,
8
“ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu suna nesa da ni.
9
A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”
10
Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane.
11
Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options