Mattiyu 15:1-9
1
Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce,
2
“Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!”
3
Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku?
4
Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’
5
Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’
6
ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku.
7
Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce,
8
“ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu suna nesa da ni.
9
A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”
Settings