Skip to content
Mattiyu 15:10-20

Mattiyu 15:10-20

10
Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane.
11
Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.”
12
Sai almajiran suka zo wurinsa suka ce, “Ka san cewa Farisiyawa ba su ji daɗi sa’ad da suka ji wannan ba?”
13
Ya amsa ya ce, “Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi.
14
Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne.In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.”
15
Bitrus ya ce, “Ka bayyana mana wannan misali.”
16
Yesu ya tambaye su ya ce, “Har yanzu ba ku gane ba ne?
17
Ba ku gane cewa duk abin da ya shiga baki yakan wuce ciki ne daga nan kuma yă fita daga jiki ba?
18
Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum.
19
Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.
20
Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options