Markus 9:7-31
7
Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!”
8
Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu.
9
Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.
10
Suka riƙe wannan zance a ɓoye tsakaninsu, suna tattaunawa ko mece ce ma’anar “tashi daga matattu.”
11
Suka tambaye shi, suka ce, “Don me malaman dokoki suke cewa, sai Iliya ya fara zuwa?”
12
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya ne, Iliya zai zo da fari, yă kuma mayar da dukan abubuwa. Don me kuma aka rubuta cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahala sosai, kuma a ƙi shi?
13
Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, kuma suka yi duk abin da suka ga dama da shi, kamar yadda aka rubuta game da shi.”
14
Da suka dawo wurin sauran almajiran, sai suka ga babban taro kewaye da su, malaman dokoki suna gardama da su.
15
Nan take da dukan mutanen suka ga Yesu, sai suka cika da mamaki, suka ruga da gudu don su gai da shi.
16
Ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi da su?”
17
Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, “Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana.
18
Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba.”
19
Yesu ya ce, “Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.”
20
Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa.
21
Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, “Tun yaushe yake haka?” Ya ce, “Tun yana ƙarami.
22
Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”
23
Yesu ya ce, “ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”
24
Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!”
25
Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, “Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.”
26
Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.”
27
Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye.
28
Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?”
29
Ya amsa ya ce, “Sai da addu’akaɗai irin wannan yakan fita.”
30
Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yă san inda suke ba,
31
gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.”
Settings