Skip to content
Markus 6:38-56

Markus 6:38-56

38
Sai ya yi tambaya ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.” Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.”
39
Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa.
40
Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin.
41
Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka.
42
Kowa ya ci, ya ƙoshi,
43
almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu.
44
Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.
45
Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron.
46
Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a.
47
Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai.
48
Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su,
49
amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu,
50
domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata. Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”
51
Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki,
52
gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.
53
Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya.
54
Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu.
55
Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake.
56
Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options