Skip to content
Markus 14:6-13

Markus 14:6-13

6
Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni.
7
Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba.
8
Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin jana’izata.
9
Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bishara ko’ina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.”
10
Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su.
11
Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi.
12
A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
13
Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options