Markus 13:5-13
5
Sai Yesu ya ce musu, “Ku lura fa kada wani yă ruɗe ku.
6
Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa.
7
Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna.
8
Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.
9
“Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu.
10
Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai.
11
Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.
12
“Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.
13
Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
Settings