Markus 10:1-12
1
Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba.
2
Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yă saki matarsa?”
3
Ya amsa ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”
4
Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yă rubuta takardar saki, yă kuma kore ta.”
5
Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka.
6
Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’
7
‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa,
8
su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya.
9
Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.”
10
Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan.
11
Ya amsa ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki.
12
In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”
Settings