Luka 23:13-25
13
Bilatus ya tara manyan firistoci, da masu mulki, da mutane,
14
ya ce musu, “Kun kawo mini wannan mutum, a matsayin wanda yana zuga mutane su yi tawaye. Na bincike shi a gabanku, ban ga a kan me kuka kawo kararsa ba.
15
Haka ma Hiridus, shi ya sa ya dawo da shi nan wurinmu. Kamar yadda ku ma kun gani, ba abin da mutumin nan ya yi, da ya isa mutuwa.
16
Saboda haka, zan yi masa bulala, in sāke shi.”
18
Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!”
19
(Barabbas yana kurkuku saboda laifin tā da hankali a birnin, da kuma don kisankai.)
20
Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu.
21
Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”
22
Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, sa’an nan in sāke shi.”
23
Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi.
24
Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu.
25
Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda tā da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Sa’an nan ya ba da Yesu ga nufinsu.
Settings