Luka 21:8-19
8
Ya amsa ya ce, “Ku lura, kada ku kuma a ruɗe ku. Gama da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi,’ da kuma, ‘Lokaci ya yi kusa.’ Kada ku bi su.
9
Sa’ad da kuka ji labarin yaƙe-yaƙe, da juye juyen mulki, kada ku tsorota. Dole ne waɗannan abubuwa su fara faruwa, amma ƙarshen ba zai zo nan da nan ba.”
10
Sai ya ce musu, “Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki zai tasar wa mulki.
11
Za a yi manyan girgizar ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama.
12
“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.
13
Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su.
14
Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku.
15
Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.
16
Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.
17
Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.
18
Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba.
19
Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.
Settings