Luka 20:27-36
27
Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa,
28
“Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’
29
To, an yi waɗansu ’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ’ya’ya.
30
Na biyun,
31
da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ’ya’ya.
32
A ƙarshe, ita macen ma ta mutu.
33
Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.”
34
Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure,
35
amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba.
36
Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne.
Settings