Skip to content
Luka 20:1-15

Luka 20:1-15

1
Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa.
2
Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?”
3
Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini,
4
baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?”
5
Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
6
Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.”
7
Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.”
8
Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”
9
Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya.
10
A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ’ya’yan inabin. Amma ’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi.
11
Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi.
12
Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje.
13
“Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’
14
“Amma da ’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’
15
Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi. “To, me mai gonar inabin zai yi da su?
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options