Skip to content
Luka 20:1-8

Luka 20:1-8

1
Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa.
2
Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?”
3
Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini,
4
baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?”
5
Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
6
Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.”
7
Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.”
8
Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options